
Aminu Abdullahi Ibrahim
An samu daidaito biyo bayan zanga-zangar kwanaki biyu da mutanen garin Jajira suka gudanar kan rufe musu hanya sanadiyar aikin gina titin jirgin kasa a Kano.
Idan za a iya tunawa al’ummar garin Jajira dake karamar hukumar Unggo sun shafe kwanaki 2 suna gudanar zanga-zanga da zaman dirshen kan zargin masu aikin gina titin jirgin kasa da rufe hanyar da ta sada garin da sauran garuruwa makwabta.

Sakamakon zanga-zangar tasu karamar hukumar Ungoggo ta kafa kwamiti da zai bibiyi al’amarin tare da samar da daidaito.
A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan Kano ta zauna da duka bangarorin da abin ya shafa da suka hada da mutanen Jajira da ma’aikatar sufuri ta tarayya da karamar hukumar Ungoggo da Hakimi da Maigari da kuma wakilan kamfanin dake gudanar da aikin.
Yayin zaman tattaunawar kamfanin ya amince zai fitar musu da hanya ta shiga garin nasu kamar yadda daya daga cikin mutanen garin ya bayyana mana.
Shima matemakin shugaban karamar hukumar Ungoggo wanda yake shugabantar kwamitin samar da masalaha Auwal Isah ya ce zasu cigaba da bibiyar lamarin dan tabbatar da cewa an samu adalci.
Auwal Isah ya kara da cewa karamar hukumar Ungoggo zata mika takarda ga gwamnan Kano domin duba yiwuwar yi musu babbar gada a garin na Jajira.
