Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya ce sama da mutane 380 aka kama, yayin kotu ta hukunta sama da 230 daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, cikin watanni biyu da ƙaddamar da yaƙin da jihar ke yi kan shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya ce gwamnatin jihar ta kafa rundunar haɗin gwiwa ta yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su a watan yulin 2026, domin ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi, harkar daba da sauran laifuka.
A cewar sa rundunar ta gudanar da samame a wuraren da ake zargin ana aikata laifuka, tare da tarwatsa wasu wuraren da ake sayarwa ko shan miyagun ƙwayoyi da kuma maboyar ’yan daba a sassa daban-daban na jihar.
Gwamna Yusuf ya bayyana yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da aikata laifuka a matsayin nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, malaman addini, iyaye da sauran al’umma, yana mai kira ga matasa da su guji miyagun ƙwayoyi da tashin hankali.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na buƙatar matasa da su mayar da hankali kan ilimi, noma, fasaha, sana’o’i da kasuwanci, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri daga al’umma da magance matsalolin da ke haddasa aikata laifuka da rashin tsaro.
