Jam’iyyar hadaka da ADC ta zargi hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, da yin aiki ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu domin lalata jam’iyyun adawa a Najeriya.
A sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce jam’iyyar ta yi watsi da fassarar da INEC ta yi kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, tana mai cewa matakin ya nuna alamun matsin lamba daga gwamnati.
Jam’iyyar ta ADC bayyana cewa, bayanin da hukumar INEC ta fitar na cike da sabani da kuma rashin daidaito da gaskiyar abin da kotu ta yanke, inda ta zargi hukumar da karkata ga bangaren gwamnati.
ADC ta ƙara da cewa, tana nazarin matakan da za ta ɗauka nan gaba, tare da kira ga mambobinta da sauran yan Najeriya da su ci gaba da tsayawa tsayin daka yayin da ake jiran mataki na gaba.
