Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniCasemiro ya fadamin zai koma Manchester United- Carlo Ancelotti

Casemiro ya fadamin zai koma Manchester United- Carlo Ancelotti

Date:

 

Ahmad Hamisu Gwale

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti, ya ce dan wasa Casemiro ya gaya masa cewa zai koma Manchester United.

A makon da muke bankwana da shi ne rahotanni suka bayyana Manchester United na zawarcin dan wasan, dan asalin kasar Brazil.

Casemiro wanda ya lashe gasar cin kofin zakarun turai biyar a tawagar Los Blancos, kuma ya kasance tare da Luka Modric da Toni Kroos a gurbi na tsakiya.

Manchester United dai tuni ta ke shirin hakura da siyan Frenkie de Jong na Barcelona, wanda hakan ka iya bata damar mika kudi fam miliyan 60 domin daukar dan wasan na Brazil.

Shin me Ancelotti ya ce bayan furucin Casemiro?

“Shakka babu munyi magana da Casemiro a wannan safiya, kuma ya ce min yana bukatar sauyin waje, da kuma fuskantar sabon kalu bale, har ma da burin samun da marmaki, kuma na fahimci dalilin sa kuma babu damuwa da hakan,’ a cewar Carlo Ancelotti.

Carlo Ancelotti Ya kara da cewa kungiyar na burin ci gaba da zaman dan wasan, amma hakan zai zama kalubale matuka, sai dai muna yi mishi fatan alkhairi da kuma fatan samun nasara a duk in da ya kasance.

Akalla dan wasa Casemiro, Luka Modric da kuma Toni Kroos sun buga wasannin karshe 10 a matsayin ‘yan wasan tsakiya, kuma duka sun lashe wasannin karshen 10 a shekarun da suka shafe tare.

Wane shiri Real Madrid ke yi na maye gurbin Casemiro?

Tuni dai kungiyar ta sayi dan wasa Aurelien Tchouameni daga Monaco akan kudi fam miliyan 68, wanda kuma ake sarai shine zai maye gurbin Casemiro idan ya tafi.

Haka kuma jimillan, kungiyar nada ‘yan wasan tsakiya da zata ci gaba da amfani da su kamar Luka Modric da Toni Kroos, da kuma matasan ‘yan wasa Federico Valverde da Eduardo Camavinga.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories