24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBuhari ya karawa malaman makaranta wa'adin ritaya

Buhari ya karawa malaman makaranta wa’adin ritaya

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shugaban kasa Buhari ya sanya hannu kan dokar karawa malaman makaranta shekarun ajiye aiki zuwa 65.

Mai taimakawa shugaban kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta amince da dokar karawa malaman wa’adin yin ritaya ne a watan Janairun bara inda kuma shugaban kasa ya aikewa majalissun dokoki na tarayya dokar a watan Yunin na bara inda bayan da suka amince da dokar ne kuma ya sanya mata hannu.

Sashin farko na dokar yace malamai a kasar nan sai sun shekara 65 zasu ajiye aiki maimakon shekaru sittin da ma’aikatan gwamnati ke ajiye aiki.

2023: Malamai su daina yiwa ‘yan siyasa addu’a don neman kudi-Muhammadu Sanusu II
Haka zalika dokar ta ce malamin makaranta zayyi ritaya ne yayin da ya shekara 40 yana aiki maimakon shekara 35 kamar sauran ma’aiakatan gwamnati.

Latest stories