Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniZa a fadada masallacin farko da aka gina a musulunci

Za a fadada masallacin farko da aka gina a musulunci

Date:

Yarima mai jiran Gado na Saudia Muhammad Bin Salman, ya kaddamar da aikin fadada masallacin annabi sallallahu alaihi wasallam na Quba dake Madina.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shafin Haramain Sharifain ya wallafa.

QubaAn nada Sheikh Nuru Khalid sabon limamin Juma’a a Abuja

Manzon Allah S.A.W ne ya dasa harsashin gina masallacin a karni na bakwai lokacin da yayi hijira daga Makka zuwa Madina inda ya yada zango a wani kauye mai suna Quba wanda ke da tazarar kilomita shida da cikin garin Madina a wancan lokaci.

Masallacin Quba shine na farko da aka gina a musulunci kuma Manzon Allah ya shafe kwanaki goma sha hudu a masallaci sa’ilin da yake jiran isowar sayyadina Ali daga garin Makkah kuma a masallacin Quba ne aka fara yin sallar Juma’a a tarihin musulunci wacce manzon Allah S.A.W yayi limanci.

Haka zalika hadisan Ahmad Ibn Hanbal dana Al’nasa’I Ibn Maja, sun rawaito cewa manzon Allah S.A.W ya ce yin sallah raka biyu a masallacin Quba daidai yake da ladan wanda yayi Umrah.

Latest stories

Related stories