Jamiyyar ADC reshen jihar nan ta kalubalanci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan hujjojin da ya bayyana na sake zabar mataimakinsa Murtala Sule Garo a zaben 2027 dake tafe.
A safiyar Litinin din nan ne gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyyana sake zabar Murtala Sule Garo amatsayin abokin takararsa a zaben badi bisa biyayya da jajircewa wajen bunkasa jihar nan.
Sai dai mai magana da yawun jamiyyar ADC a nan Kano Kwamrade Sa’idu Bello, yace akwai bukatar Gwamnan ya fito yayi bayani dalla-dalla kan sauyin da matemakin gwamnan ya samar.
Tuni dai harkokin siyasa ke cigaba da daukar dumi a jihar nan tsakanin jam’iyun siyasa daban-daban.
