Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana Murtala Garo a matsayin abokin takararsa na zaɓen 2027
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Litinin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan yayin wata ganawa da masu riƙe da muƙaman siyasa na gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda aka gudanar a masaukin gwamnatin Jihar Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon biyayya, jajircewa da kuma ƙoƙarin da Murtala Garo ya nuna wajen bunƙasa Jihar Kano tun bayan hawansa kan muƙamin mataimakin gwamna.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da kuma magoya baya da su ci gaba da bayar da haɗin kai da jajircewa domin ci gaba da gina nasarorin da gwamnati ta samu tare da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.
