Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 61 a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa sun kammala sauke Alƙur’ani Mai Tsarki a wani shiri na gyaran hali da koyar da addini.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar, fursunonin da suka kammala shirin sun haɗa da maza 55 da mata shida.
Sanarwar ta ce da dama daga cikin waɗanda suka sauke Alƙur’anin ba su da cikakken ilimin karatu da haddar Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali, amma ta hanyar koyarwa da horo na musamman sun samu nasarar kammala haddarsa.
Domin ƙarfafa musu gwiwa, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tare da haɗin gwiwar gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation sun rabawa waɗanda suka kammala karatun kayan tallafi da suka haɗa da sabbin kaya, katifu, barguna da kuma tallafin kuɗi domin sauƙaƙa musu komawa cikin al’umma bayan sun kammala zaman gidan gyaran hali.
Mai kula da Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yabawa Babban Kwanturolan Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagorancinsa da kuma ƙoƙarin da yake yi na bunƙasa shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i da tarbiyya a gidajen gyaran hali na faɗin ƙasar nan.
