Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kan yawan kiran Shugaba Bola Tinubu da sunansa na farko.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce ko da Atiku ya kira Shugaba Tinubu da Bola ko Adekunle, hakan ba zai sauya matsayinsa na shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Najeriya ba.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce ba zai bi sahun Babachir Lawal wajen kiran Atiku da Kachalla ba, yana mai cewa zai ci gaba da kiransa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Haka kuma, Shettima ya kwatanta yunƙurin Atiku na neman shugabancin Najeriya sau da dama da na tsohon Firaministan Kenya, Raila Odinga, wanda ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasa.
A wani ɓangare na jawabinsa, Shettima ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, kan wasu manufofinsa na tattalin arziki da kuma ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Sai dai ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da su guji cin mutuncin abokan hamayyarsu, su mayar da hankali wajen gabatar da hujjoji da ƙididdiga.
