Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shekarar 2027 ba, domin mayar da hankali kan gudanar da ayyukan gwamnati da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a birnin Abuja.
Shugaban Ƙasar ya buƙaci mambobin kwamitin da su ɗauki nauyin yaɗa manufofi da saƙonnin jam’iyyar zuwa ga ’yan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya ce ya amince da shawarar cewa kada ayyukan yaƙin neman zaɓe su zama abin da zai hana shi sauke nauyin da ke kansa na jagorantar ƙasar.
A cewarsa, Najeriya na buƙatar kulawarsa a wannan lokaci, musamman wajen magance ƙalubalen tattalin arziki da sauran matsalolin da ke fuskantar al’umma.
Wannan mataki na nuna cewa Tinubu na son barin gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓen a hannun shugabannin kwamitin, yayin da shi kuma zai mayar da hankali kan gudanar da mulki.
