Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Hukumar ICPC ta saki tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, idan har yana da ikon ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa umarni kan yadda suke gudanar da ayyukansu, kamar yadda ya yi kan Hukumar EFCC.
A cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce umarnin da Shugaba Tinubu ya bai wa EFCC na janye matakin da ya shafi umarnin kotu na rufe asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun ya nuna cewa fadar shugaban ƙasa na da tasiri kai tsaye kan ayyukan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa.
Atiku ya bayyana cewa akwai buƙatar fadar shugaban ƙasa ta fito fili domin nuna ikirarin cin gashin kan waɗannan hukumomi a ƙarƙashin gwamnatins sha gaskiya ba ne.
Ya kara da cewa janye matakin rufe asusun Gwamnatin Jihar Osun na iya taimakawa wajen kauce wa ƙarin tangarda ga shirye-shiryen gudanar da zaɓe a jihar.
