Jam’iyyar APC mai mulki ta musanta rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaɓenta na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 domin sake duba shi.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya ce rahotannin jita-jita ne, yana mai cewa duk wani sauyi da za a yi wa jerin sunayen za a sanar da shi a hukumance.
Morka ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da jaridar TheCable a safiyar Talata, kan rahotannin cewa jam’iyyar ta janye jerin sunayen sakamakon cece-kuce game da wasu mutanen da aka saka da waɗanda aka bari a baya.
Ya ce, “Jita-jita ba labari ba ce. Akwai labaran ƙarya, sannan akwai sahihan labarai.”
Ya ƙara da cewa, “A halin yanzu babu wanda zai bayar da wani sabon jerin sunaye. Amma idan akwai dalilin sabunta jerin, za a sanar da hakan ta hanyar da yakamata.”
APC ta sanar da kwamitin yakin neman zaɓen a ranar Asabar, inda Shugaba Bola Tinubu yake matsayin shugaban kwamitin.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, an naɗa su a matsayin mataimakan shugaban kwamitin.
Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, shi ne Darakta-Janar, yayin da Gwamnan Imo kuma shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma, aka naɗa sakatare.
Sai dai tsarin kwamitin ya jawo cece-kuce, musamman kan sanya wasu jami’an gwamnati da kuma wasu mutanen da ake zargi da aikata laifukan cin hanci da rashawa.
Daga cikin waɗanda aka ambata a cikin jerin akwai tsohuwar Ministar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Betta Edu; tsohuwar shugabar hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund, Ngozi Olejeme; shugaban Hukumar Tara Haraji ta Najeriya, Zacch Adedeji; da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Tanimu Yakubu.
A ranar Litinin ne rahotanni suka bayyana cewa ana duba jerin sunayen ne saboda damuwar da wasu daga cikin waɗanda aka saka suka nuna na rashin sanya wasu manyan ’yan jam’iyyar.
Sai dai Felix Morka ya ce ba shi ne mutumin da ya dace ya mayar da martani kan koke-koken ’yan jam’iyyar game da waɗanda ba a saka cikin kwamitin ba.
