Gwamnatin Kano ta ce ta samu gagarumar nasara a fannin harkokin kiwon lafiya a matakin farko cikin shekaru uku da suka gabata, sakamakon zuba jari da ta yi wajen inganta cibiyoyin lafiya, samar da magunguna da kayan aiki, da ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar al’umma musamman a yankunan karkara.
Shugaban Hukumar kula da lafiya Matakin farko ta Kano, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai.
Sai dai Farfesa Salisu ya ce duk da nasarorin da aka samu a ɓangaren, har yanzu akwai gibin ma’aikatan lafiya, inda ya ce hukumar na da ma’aikata kusan dubu shida, alhali ake bukatar akalla dubu goma sha daya domin samar da cikakkun ayyukan kiwon lafiya a kananan hukumomi 44 na jihar.
Farfesa Salisu ya ce hukumar za ta ci gaba da hada kai da sauran masu ruwa da tsaki wajen inganta ayyukan kula da lafiya, tare da wayar da kan al’umma domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga daukacin al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Farfesa Salisu na tabbatar da shirin gwamnatin Kano na ci gaba da kyakkyawan tsari da samar da yanayin kula da lafiya a matakin farko na jihar domin samar da kulawar lafiya ga al’ummar Kano.
