Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta ta ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa da ƙasar Birtaniya domin bunƙasa ci gaba a fannoni daban-daban.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta ne ya bayyana hakan yayin da tawagar Jakadancin kasar Birtaniya a Najeriya ta kai masa ziyara.
Da yake jawabi yayin karbar bakin, Mataimakin Gwamnan ya ce ziyarar na nuna ƙudirin ɓangarorin biyu na ƙarfafa haɗin gwiwa, bunƙasa alakar jihar Kano da kasar Birtaniya da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin mulki da ci gaba.
Mataimakin gwamnan ya ce bangarorin biyu suna iya cimma manyan nasarori ta hanyar haɗin gwiwa bisa amincewa, gaskiya da ɗaukar nauyi tare, yana mai jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau domin samar da gudunmawa wajen gina Kano da cigaba da bunƙasa tattalin arziki.
Tun da farko, shugabar tawagar ta kasar Birtaniya kuma Shugabar haɗin gwiwar ci gaba ta hukumar jakadancin Birtaniya, Cynthia Rowe, ta ce sun zo Kano ne domin ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tare da mayar da hankali kan muhimman fannoni guda uku da suka haɗar da tsaro da zaman lafiya, inganta harkokin lafiya, ilimi, noma da kyakkyawan shugabanci.
