Sanata Mohammed Ali Ndume bayyana cewa, ƙananan yara 42 ne mayaƙan kungiyar Boko Haram suka sace a Makarantar Firamare da kuma Ƙaramar Sakandiren a garin Mussa da ke Ƙaramar hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.
Sanata Ali Ndume, wanda ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, ya ce ya samu bayanin ne daga mahukuntan makarantar da kuma shugabannin al’umma a Asabar din nan.
Da sanyin safiyar ranar Juma’ar data gabata ne mayaƙan Boko Haram suka kai hari makarantar, inda rahotanni suka ce sun yi awon gaba da wasu yara da ba a tantance yawansu ba.
Ya bayyana cewa sace ɗaliban makarantar ya fi tayar da hankali, domin an yi garkuwa da yaran ne yayin da suke aji domin ɗaukar darusi a makarantar.
Saboda haka, ya roƙi dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Haɗin Kai da sauran hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen nema da ceto waɗanda aka sace.
Ya kuma bayyana cewa sace yaran makarantar an shirya shi ne bayan wasu hare-hare da suka yi sanadin mutuwar sama da mutum shida tare da lalata gidaje da dama.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yankunan Chibok da sauran hare-haren da aka kai a yankin Sanatan Borno ta Kudu.
Mazabar Ndume na ci gaba da fuskantar hare-hare a baya-bayan nan, musamman harin da aka kai wasu ƙauyukan Chibok na a ranar Alhamis din data gabata inda aka kashe mutane da dama.
