Gwamnatin Jihar Kano ta fito fili ta wanke tsohon Shugaban Ma’aikatan Jiha, Abdullahi Musa, daga zargin karkatar da Naira biliyan 1.5 na albashin ma’aikata, inda ta bayyana cewa babu hannun wani jami’in gwamnati a cikin lamarin.
Sakataren Gwamnatin Jiha, Umar Faruk Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin taron karrama ma’aikata na Ranar Ma’aikata ta duniya da Nigeria Labour Congress da Trade Union Congress suka shirya a Fadar Gwamnati da ke Kano a ranar Juma’a.
Ibrahim ya ce binciken da kwamitin gwamnati ya gudanar, tare da goyon bayan wani kamfanin bincike mai zaman kansa, ya tabbatar da cewa sabanin da aka samu ya samo asali ne daga cire kudade sama da kima da kamfanonin bayar da lamuni suka yi daga albashin ma’aikata.
A cewarsa, wadannan kamfanoni sun rika cire kudade fiye da adadin da ya kamata daga bashin da ma’aikata suka karɓa, lamarin da ya haifar da wannan cece-kuce.
“Rahoton kwamitin, wanda wani kamfanin bincike mai zaman kansa ya tabbatar, ya nuna karara cewa babu wani jami’in gwamnati da ke da hannu a cikin lamarin. Matsalar ta samo asali ne daga masu bayar da lamuni da suka yi cire kudade fiye da kima daga albashin ma’aikata,” in ji shi.
SSG ya tabbatar wa ma’aikata cewa za a mayar da duk kudaden da aka cire ba bisa ka’ida ba ga wadanda abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa tuni kamfanonin sun amince za su biya kudaden.
Haka kuma ya sake jaddada kudirin gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf na kare jin dadin ma’aikata da kuma kare hakkokinsu na kudi a fadin jihar.
Wannan karin haske ya zo ne bayan umarnin gwamnan da ya bayar na gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin cewa sama da Naira biliyan 1.5 na albashin ma’aikata ya bace a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ma’aikata.
Gwamna Yusuf ya bayar da wannan umarni ne a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2026 a Kano, bayan da shugaban NLC na jihar, Kabiru Inuwa, ya gabatar da zargin.
“In ji gwamnan, ‘Na ji zargin cewa tsohon Shugaban Ma’aikata ya karkatar da kusan Naira biliyan 1.5. Nan take na kira Sakataren Gwamnatin Jiha tare da ba da umarnin kafa kwamitin bincike,’” in ji shi.
Ya kuma sha alwashin cewa duk wanda aka samu da laifi a lamarin, za a hukunta shi bisa doka tare da tilasta masa mayar da kudaden.
Sai dai sabon bayani daga SSG ya kawo karshen cece-kuce, inda ya tabbatar da cewa tsohon Shugaban Ma’aikata ba shi da hannu a lamarin, tare da mayar da laifi gaba ɗaya kan masu bayar da lamuni.
