Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiDSS ta gurfanar da wata mata da aka kama da bindigogin harba...

DSS ta gurfanar da wata mata da aka kama da bindigogin harba rokoki a Wudil dake Kano.

Date:

An ci gaba da shari’ar wata mata da aka kama da bindigogin harba rokoki guda uku a kusa da Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin ‘yan Sanda da ke Wudil a nan Kano.

Aminiya ta ruwaito hukumar DSS ce ta gurfanar da matar wadda ‘yar asalin Karamar Hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara ce.

A zaman kotun na ranar Litinin, wadda ake zargin ta shaida wa kotu cewa tana tsaka da barci ne jami’an DSS suka je suka kama ta suka tsare ta.

A cewarta, jami’an hukumar sun azabartar da ita tare da tursasa mata cewa ta amsa ita ce mai makaman da ake zargi, amma ta ki amsawa.

Bayan sauraron bayanan ne kotu ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan yuni da muke ciki.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...