Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa ta kammala biyan dukkan kuɗaɗen da suka rage ga maniyyatan Hajjin shekarar 2026 waɗanda suka riga suka biya kuɗin farko.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce an riga an kammala biyan kuɗaɗen ga maniyyata cikin rukuni-rukuni har guda biyar.
A sanarwar da mai magana da yawun hukumar Suleiman A Dederi ya fitar yace a baya an kayyade kuɗin Hajji a kan naira miliyan 8 da dubu dari 500 amma daga bisani aka rage shi zuwa naira miliyan 7 da dubu dari 696.
Ya ce bambancin da ke tsakanin waɗannan kuɗaɗe an mayar da shi gaba ɗaya ga dukkan maniyyatan da abin ya shafa.
Alhaji Matawalle ya ƙara da cewa duk wani maniyyaci da bai karɓi nasa kuɗin ba ya gaggauta tuntuɓar bankinsa ko kuma jami’an Hajji a ƙaramar hukumar da yake domin warware matsalarsa cikin sauƙi.
Ya jaddada cewa hukumar ta cika alƙawarin da ta ɗauka na tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen kula da harkokin maniyyata.
