Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano.
An rantsar da Garo ne a ranar Talata bayan nadinsa domin cike gurbin da ya biyo bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.
Sakon taya murnar na Tinubu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.
Shugaban ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su bai wa gwamna da mataimakinsa cikakken goyon baya domin tabbatar da ingantaccen shugabanci.
Haka kuma Tinubu ya shawarci sabon mataimakin gwamnan da ya yi aiki kafada da kafada da gwamnan domin hanzarta ci gaban jihar.
