Wani matashi mai suna Nura Ribadu ya rasa ransa bayan wani hari da wasu gungun yan daban siyasa suka kai masa a harabar Asibitin Kano Medical Center (KMC) da ke kan titin Race Course a birnin Kano.
Rahotannin farko sun ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan rantsar da sabon Mataimakin gwamnan jihar Kano.
Rahotanni da ke yawo sun yi iƙirarin cewa mamacin na da alaƙa da tafiyar siyasar Sanata Barau I. Jibrin, yayin da wasu ke zargin mutanen da suka kai harin ma na ɗauke da alamun goyon siyasar Murtala Garo.
