Hukumar dakile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC, ta bayyana damuwa kan yadda mace-macen da cutar zazzabin Lassa ke haddasawa ke ƙaruwa a faɗin ƙasar, inda ta danganta hakan da jinkirin neman magani da kuma rashin zuwa Asibiti da wuri.
A cikin sabon rahoton mako na 18 na shekarar 2026, wanda ya shafi tsakanin 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu, hukumar ta ce mutane 191 sun mutu sakamakon cutar tun daga farkon shekarar nan.
Rahoton ya nuna cewa adadin mace-macen ya kai kashi 24.6 cikin ɗari, idan aka kwatanta da kashi 19.2 cikin ɗari a irin wannan lokaci a shekarar 2025.
Hukumar ta ce yawan waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya ƙaru daga mutum tara a mako na 17 zuwa mutum 22 a mako na 18, inda aka samu sababbin masu cutar a jihohin Ondo, Edo da Plateau.
Rahoton ya kuma bayyana cewa jihohi 23 da ƙananan hukumomi 106 sun samu tabbatattun masu cutar a shekarar 2026.
Jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benue da Edo ne suka fi yawan masu kamuwa da cutar, inda suka kai kashi 84 cikin ɗari na dukkan masu cutar a ƙasar.
A cewar hukumar, matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da aka kuma samu karin ma’aikacin lafiya guda ɗaya da ya kamu da cutar.
