Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Isra’ila da Lebanon sun amince su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanisu, wadda ta kamata ta ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.
Amurka ta ce yanzu an tsawaita wa’adin yarjejeniyar da kwana 40 bayan shiga tsakani da gwamnatin Donald Trump ta yi.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa yarjejeniyar wadda ta fara aiki a watan jiya ba ta hana Isra’ila kai hare-hare a wuraren da ta ce suna da alaƙa da mayaƙan Hezbollah mai samun goyon bayan Iran.
Ita ma dai Hezbollah ta ci gaba da kai hare-hare ta hanyar jefa rokoki a arewacin Isra’ila, sannan ko yanzu Hezbollah ba ta cikin waɗanda Amurka ta zauna da su.
