Bangaren jam’iyyar PDP da Tanimu Turaki ke jagoranta ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.
Sakataren Yada Labarai na Kwamitin Rikon Kwarya na PDP na Ƙasa, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wanda ya tabbatar da Adebayo Adedamola a matsayin ɗan takarar bangaren Turaki.
Kotun ta kuma umarci Hukumar INEC da ta saka tambarin PDP a takardun zaɓen, bayan da ta tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani tare da miƙa sunan wanda ya yi nasara ga hukumar.
Sai dai Ememobong ya ce, duk da nasarar da bangaren suka samu a kotu, jinkirin da aka samu ya hana ɗan takarar PDP damar gudanar da yakin neman zaɓe yadda ya kamata.
Ya ce, bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, bangaren PDP ɗin ya yanke shawarar goyon bayan Adeleke, tare da yin kira ga mambobin jam’iyyar da su kaɗa kuri’a, su kare kuri’unsu, sannan su tabbatar da an ƙirga su.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji tashin hankali da kuma ƙoƙarin samun nasara a zaɓe ta kowace hanya, yana mai cewa sakamakon zaɓe ya kamata ya kasance cikakken abin da jama’a suka zaɓa cikin ‘yanci
