Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta yi wa Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, tambayoyi kan zargin alaƙarsa da badakalar hukumar bunƙasa zuba jari ta kasashen waje (PFIPC), wadda gwamnatin tarayya ta ce ba ta da sahihanci.
Lauyan Gbajabiamila, Jiti Ogunye, ya bayyana cewa ya amsa gayyatar ICPC a ranar Litinin, inda ya ba da bayanansa tare da amsa tambayoyin masu bincike kafin ya koma bakin aikinsa.
A ranar 2 ga Yuli, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.
Ana zargin Adeniyi Adeyemi, wanda ake cewa ya jagoranci PFIPC, da ikirarin cewa Gbajabiamila ne ya ba shi takardar naɗi, zargin da shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban kasar ya musanta. Adeyemi ya kuma zargi Gbajabiamila da karɓar Naira miliyan 400 ta hannun wani da kuma neman ƙarin Naira miliyan 200 domin tabbatar da naɗinsa.
Sai dai ‘yansanda sun gurfanar da Adeyemi kan zargin jabun takardu da kwaikwayon jami’in gwamnati, tare da kama shi bayan kotu ta bayar da umarnin cafke shi saboda rashin halartar shari’a.
Duk da cewa PFIPC ba ta da wata kafa ta doka, an ce ta yi aiki kamar hukuma ta gwamnati, har ma aka ware mata kuɗi a kasafin kuɗin 2026.
