Zauren hadin kan malamai da kungiyoyi na jihar Kano ya jinjinawa Gwamnatin Kano.
Malaman karkashin jagorancin Farfesa Musa Muhammad Borodo, sun yi jinjinar ne kan ayyukan kwashe kananan yara da ke gararamba a tituna tare da ba su kulawa ta musamman.
Sun kuma yi hakan ne bayan kai ziyarar gani da Ido sansanin kula da yaran.
Farfesa Borodo ya jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin al’umma da hukumomi domin ganin shirin ya yi nasara.
A jawabinsa, Sheikh Abdulwahab Abdullah ya bukaci iyaye da su kara kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.
“Hakkin ilimi da tarbiyyar yara nauyi ne da ya rataya a wuyan iyaye”. Inji shi.
Malaman sun kuma jinjinawa shugaban Hukumar Hisbah Sheikh Ibrahim Daurawa bisa kokarinsa na ganin an kwashe yaran daga kasuwanni da tashoshin mota da gadoji.
Ya kuma tabbatar da cewa za su ba da duk goyon bayan da ake bukata don cigaban shirin.