Jamiyyar NDC ta kasa ta kawo karshen takaddamar shugabancin reshenta na nan Kano, ta hanyar nada Hussaini Isah Mairiga a matsayin shugabanta, domin jan ragamar ta wajen samun nasara a zaben 2027 dake tafe.
Yayin wani taro da shugabannin jamiyyar karkashin jagorancin mataimakin shugabanta na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso yamma, Muhammad Sabo Bakin Zuwo, an cimma matsayar tabbatar masa da kujerar biyo bayan kuwwa da ya yi na zargin Kwankwaso da tawagarsa da neman mayar da shi dan kallo a shugabancin jamiyyar.
Cimma wannan matsaya na nufin cewa yanzu jamiyyar anan Kano cikin aminci take, yayin da shirye shiryen Kwankwaso da Peter Obi na neman kawo karshen mulkin Tinubu na jamiyyar APC ke ci gaba da kara kankama.
To amma ko yaya masana siyasar ke ganin yanayin tafiyar siyasar, duba da a yan kwanaki mutanen biyu suka koma ADC yanzu kuma sun sake fita tare da komawa NDC.
Farfesa Kamilu Sani Fage daga jami’ar Bayero na ganin cewa hakan ba komai yake nunawa ba face yadda siyasar yanzu ta koma me mutum zai amfana sama da me zai amfanar ga alumma.
