Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin samar da gurin sake sarrafa shara mai faɗin hekta 100 domin bunƙasa tattalin arziki da sake amfani da su wato renewable energy, don samar da ayyukan yi. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Shara ta Kano, REMASAB, Malam Abubakar Ahmad, ya fitar a ranar Talata 30 ga Yuni, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa Shugaban Hukumar, Dakta Muhammad S. Khalil, ya ce gurin zai zama cibiyar da za ta haɗa kamfanonin sake sarrafa shara, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki, tare da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa domin gudanar da ayyukansu.
Ya ƙara da cewa hukumar ta tsara masu tattara shara da masu saye da sayar da shara cikin ƙungiyoyin haɗin gwiwa, sannan ta horas da mata 160 kan sake amfani da shara tare da ba su kayan kariya da kayan aiki domin inganta ayyukansu.
