Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoYanda muhawarar yan takarar gwamna a Kano ta kasance

Yanda muhawarar yan takarar gwamna a Kano ta kasance

Date:

Hafsat Nasir Umar

 

An gudanar da muhawarar ‘yan takarar gwamnoni na jam’iyu daban-daban a jihar Kano da kafar yada labarai ta BBC Hausa ta shirya.

 

Muhawarar da ta shafe tsawon awa biyu ana gudanarwa ta tabo al’amura daban-daban da suka shafi batun tsaro, lafiya, ilimi, aiyuka, matasa da mata da kuma kananan yara.

 

Yan takarar da suka fafata sun hada da dan takarar jam’iyar APC kuma mataimakin gwamnan jihar Kano Nasir Yusuf Gawuna, Abba Kabir Yusuf na NNPP, Salihu Tanko Yakasai na PRP, Sha’aban Sharada na ADP da kuma Muhammad Abacha na PDP.

 

Da yake jawabi Dr Nasiru Yusuf Gawuna yayi alkwarin yaye matasan da suka koyi sana’a a cibiyoyin koyar da sana’a da ake da su a jihar.

 

Shi kuwa dan takarar gwamna na PRP Salihu Yakasai yayi alkawarin warware matsalar tsaro tun daga mazabu da unguwanni.

 

A nasa bangaren Sha’aban sharada na ADP yayi alkawarin daukar samfurin kasar kowacce karamar hukuma domin sanin irin noman da ya dace da ita da kuma kirkiro da karin madatsun ruwa domin bunkasa noman rani.

 

Shi kuwa Mohammad Abacha na PDP yace idan yayi nasara a zaben na bana zai rika bayar da kwangila ga ‘yan asalin jihar Kano maimakon ‘yan wasu jihohin ko ‘yan kasashen waje.

Latest stories

Related stories