Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano ta kama dubban...

Hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano ta kama dubban mutane sanadiyar karya ka’idojin tuki

Date:

Hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa a jihar Kano ta kama mutane 11,557 da laifin karya dokokin tuki a shekarar 2022.

 

Shugaban hukumar Zubairu Mato ne ya shida hakan yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Juma’a.

 

Ya ce wadanda aka kama din sun aikata laifuka 13,718 ciki harda kin mallakar lasisin tuki, gudun wuce kima da kuma rashin yiwa lambar mota rajista.

 

Ya kara da cewa hukumar ta kama motoci 8,700 daga Disamban 2022 zuwa yanzu da basu da lambobi masu rajista.

 

Zubairu Mato yace an samu raguwar hadurra a shekarar data gabata idan aka kwatanta da wacce ta gabaceta.

Ya gargadi iyaye dasu daina barin yara masu kananan shekaru suna tuki domin gujewa afkwuwar hadurra a akan tituna.

Latest stories

Related stories