Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYajin Aikin ASUU: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar da gwamnatin tarayya ta...

Yajin Aikin ASUU: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da ASUU

Date:

Shehu Usman Salihu

 

A zaman farko, kotun masana’antu ta Ƙasa ta ɗage shari’ar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan nan na Satumba da muke ciki.

 

Mai shari’a Polycap Hamman ta ɗage sauraron shari’ar don baiwa ɓangarorin biyu damar shigar da bayanan da su ka dace na ƙarar.

 

Kakakin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, Olajide Oshundun, ya bayyana cewa ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ne ya miƙa batun ga magatakardar kotunan masana’antu ta kasa, inda ya ƙara da cewa daga nan ne gwamnati ta garzaya kotun.

 

Ya kara da cewa ma’aikatar ta roƙi kotun da ta baiwa ASUU umarnin janye yajin aiki, yayin da ake kokarin shawo kan rikicin.

 

Idan za’a iya tunawa ASUU ta tsunduma yajin aikin ne tun a watan Fabrairun shkarar nan ta 2022, wanda ya kai ga rufe jami’o’in gwamnati na tsawon watanni takwas zuwa yanzu.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories