Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciCefanar da kotu, filin Mahaha:Abba Kabir ya maka Ganduje a Kotu

Cefanar da kotu, filin Mahaha:Abba Kabir ya maka Ganduje a Kotu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyar NNPP Abba Kabir Yusuf ya yi karar gwamnatin Kano Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu bisa siyar da filin wasa na mahaha da kuma katangar filin wasa na Sani Abacha dake unguwar kofar mata.

 

Abba Kabir ya shigar da karar ne karkashin wasu lauyoyi, inda ya zargi gwaman da cefanar da wasu kotunan musulunci biyu a nan Kano.

 

Sauran wadanda  ake karar sun hada da kwamishinan shari’a na jihar Kano da hukumar kasa da safayo.

 

Da ya ke zantawa da Premier Radio a madadin Abba Kabir Lauyansa Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurci ya zargi gwamnan da cefanar da wuraren ne saboda son rai da biyan bukatar kashin rai.

 

Ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na wuce gona da iri wajen siyar da irin wadannan wurare masu amfani ga al’ummar jihar Kano.

 

Baya ga wannan kuma masu karar sun yi korafi kan siyar da wasu kotunan shari’ar musulunci zuwa ga wasu dai-daikun mutane ko kuma masu zaman kansu, wanda shima suke ganin hakan ya sabawa dokar kasa.

 

Masu karar dai sun shigar da ita ga babban  babban mai shari’a na Kano, Justice Nura Sagir, wanda kuma ya sanya ranar 10 da 11 ga  Nuwamba domin fara sauraran karar.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...