Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMutuwar sarauniyar Ingila babban rashi ne ga Duniya-Sarkin Kano

Mutuwar sarauniyar Ingila babban rashi ne ga Duniya-Sarkin Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II a matsayin babban rashi ga Duniya.

 

Sarkin ya bayyana haka ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai ofishin jakadancin Ingila da ke Abuja.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran masarautar Abubakar Bakarabe Kofar Na’isa ya fitar ranar Litinin.

 

Kofar Na’isa ya ce Sarkin ya nuna alhininsa ga rasuwar Sarauniyar.

 

Ya ce rashin nata ba wai rashi ne ga Ingilawa kawai ba, harma da duniya baki daya.

 

Ya kuma yi fatan wanda ya gajeta zai dora daga inda Sarauniyar ta tsaya, musamman bangaren kyawawan ayyukanta.

 

Amakon da ya gabata ne dai saruniya Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.

 

Haka kuma an sanaya ranar Litinin 19 ga Satumba a matsayin ranar da za a yi mata jana’iza.

Latest stories

Related stories