Dan wasa Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan zura kwallo a wasan da kungiyarsa ta Al Nassr ta doke Al Shabab da ci 3-2.
Wasan wanda dandazon ‘yan kallo suka nuna farin cikinsu da yadda shahararren dan kwallon kafar ya rusuna ya yi sujjada a wasan da ya gudana ranar Talata.
Yanzu haka dai Al Nassr na da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta Saudiyya.
Ana dai yin sujjada ne domin nuna godiya da girmamawa ga Allah bisa wata ni’ima da ta samu bawa.

Dan kasar Portugal Ronaldo ya ci wa Al Nassr kwallo ta uku a minti na 59 kuma ya yi sujjada a filin wasa na KSU da ke Riyadh.
Kuma nan take ‘yan kallo suka barke da sowa da murna bisa abin Ronaldo da ya y a wasan da ya gudana.
‘Yan wasan Al Nassr Anderson Talisca da Abdurrahman Garib kowane ya zura kwallo daya, yayin da Cristian Guanca ya ci wa Al Shabab abin da ya sa aka tashi da ci 3-2.
Yanzu Al Nassr tana da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta kasar Saudiyya.