Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniKatsina United ta samu damar buga gasar Super 8 ta Kasa

Katsina United ta samu damar buga gasar Super 8 ta Kasa

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, ta samu damar tsallake gasar kwararru ta kasa NNL bayan do ke NAF Fc da ci 3-1 a karshen mako.

Kungiyar wadda akewa take da Chanji Boys, yanzu itace a matakin farko a rukunin A2 da take a gasar ta NNL, da maki 20.

Katsina United wadda ta buga wasanni Takwas, ba tai rashin nasara a duka wasannin ba, kuma yanzu haka wasanni biyu suka rage a kammala gasar ta shekarar 2022/2023.

Hakan da ke nuni da cewa, idan Katsina United ta kasance a matakin farko ko mataki na biyu a wasannin share fage na Super 8, to tabbata zata koma gasar Firimiya ta kasa NPFL a kakar Wasanni Mai zuwa.

A jumlace a wasanni Takwas da Yan wasan na Chanji Boys suka buga, suna yi nasarar wasannin gida Biyar, da nasara a wasan waje daya, da kuma canjaras biyu a wasannin waje.

Mai horar da kungiyar ta Katsina United Usman Abdallah da ya ke zantawa da Ahmad Hamisu Gwale ya ce, wannan nasara ta biyo bayan yadda kungiyar ta mayar da hankali domin cimma nasarar abin da ke gabansu.

Yana mai cewa abin da ya ke gabansu shi ne, samun nasarar dawowa gasar Firimiya ta kasa NPFL a kakar wasanni mai zuwa.

Katsina United Fc na shirin buga wasanni biyun da suka rage Mata a rukunin na A2 Northern Conference da City Fc da kuma kungiyar Green Beret Fc.

Latest stories

Related stories