Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniAn soke jankatin da aka bawa Vinicius na Madrid

An soke jankatin da aka bawa Vinicius na Madrid

Date:

Rahotanni sun bayyana an soke jankatin da aka bai wa Vinicius Junior a wasan Real Madrid da Valencia na karshen mako.

Da fari dai alkalin wasa Ricardo de Burgos Bengoetxea ya bawa Dan wasan kasar Brazil Vinicius jankati, kafin daga bisani Kwamitin alkalan wasanni na Sifaniya RFEF sun soke hukuncin.

Nau’rar taimakawa alkalin wasa ta VAR ce dai ta gano Vinicius na kalubalantar Dan wasan Valencia Hugo Duro, abin da ya janyo hatsaniya a wasan.

Bayan da aka gudanar da bincike yanzu haka Vinicius an gano ba shida laifi kuma zai buga wasan Real Madrid da Rayo Vallecano a gasar La Liga a wannan Larabar.

Kuma hukuncin da RFEF suka zartar ya nuna yadda aka dakatar da hana magoya bayan Valencia shiga filin wasa har na wasa biyar.

Kuma anci tarara kungiyar kudin da ya kai Yuro miliyan 45,000 kwatan kwacin Dala miliyan 39,536 bayan Zargin cin zarafin Vinicius.

Haka ma dai Yan sanda a kasar ta Sifaniya sun kama wasu mutane uku magoya bayan kungiyar ta Valencia bisa zarginsu da cin zarafin dan wasan Vinicius Junior ta hanyar kalaman wariyar launin fata.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...