Fitaccen mai sharhi kan harkokin wasanni a nan Jihar Jabir Hassan, ya sanar da yin murabus daga aikin shi na mataimakin mai horar da yan wasan First Bank.
Murabus din Jabir Hassan na zuwa ne nan take ne, bayan da aka kammala gasar da aka shirya tsakanin yan wasan bankunan jihar Kano.
Matakin wanda ya bayyana ya yi shi ne domin samun damar ci gaba da harkokin da suke gabanshi, musamman bayar da gudunmawa ga harkokin wasanni.
A shekarar da ta gabata ne 2022, Jabir Hassan ya fara aikin horar da yan wasan kungiyar na First Bank.
Sai dai kawo yanzu tuni ya sanar da yin murabus na ci gaba da aikin da ya shafe watanni yana gudanarwa.
Tuni dai aka kammala gasar da aka sanya mai taken Banker Game wanda kungiyar ta First Bank ta Kare a matakin kusa da karshe wato Semi final.
Jabir Hassan dai na guda daga cikin masu sharhi kan harkokin wasanni a wasu daga cikin kafafen yada labarai da ke nan Kano.
