Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗa kai wajen yin Allah wadai da hare-haren kyamar baƙi a Afirka ta Kudu.
Ya bukaci haka ne a madadin Shugaba Bola Tinubu yayin taron ƙoli na ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a Freetown, babban birnin Saliyo.
Shettima ya ce ya kamata a miƙa batun ga Tarayyar Afirka domin ɗaukar matakin da ya dace.
A cewarsa, Najeriya da sauran ƙasashen Afirka sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa gwagwarmayar neman ‘yancin kai da kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.
