Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bangaren ilimi ne zai samu kaso mafi tsoka a cikin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027.
Kwamishinan Ma’aikatar, Musa Suleiman Shanono, ne ya bayyana hakan yayin zaman karɓar bayanan kasafin kuɗi na ma’aikatun gwamnati da hukumomi, wanda ya gudana a yau Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan.
Zaman ya samu halartar Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, tare da wakilan hukumomi da cibiyoyin ilimi daban-daban, ciki har da Jami’ar Northwest Kano, Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kano Polytechnic da Kwalejin Legal.
Sauran hukumomin sun haɗa da SUBEB, da hukumar dake kula da Ilimin Manyan makarantun sakandire KSSSSMB da dai sauransu.
Kwamishina Musa Suleiman Shanono ya jagoranci zaman ne tare da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Haj. Umma Dallatu, da Daraktocin Ma’aikatar, a wani mataki na tattara buƙatu da bayanan da za su taimaka wajen tsara kasafin kuɗin shekarar 2027.
