Ƙasar Saudiyya ta amince da ƙarin guraben mahajjata 10,000 ga Najeriya domin aikin Hajjin shekarar 2027.
Ƙarin guraben ya sa adadin da Najeriya za ta samu ya tashi daga mahajjata 50,000 zuwa 60,000.
Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sanar da hakan, inda ta ce ƙarin guraben ya biyo bayan tattaunawa da ƙoƙarin diflomasiyya da gwamnatin Najeriya ta yi da hukumomin Saudiyya.
NAHCON ta ce za a bai wa hukumomin kula da aikin Hajji na jihohi gurabe 7,500 daga cikin ƙarin guraben, yayin da sauran 2,500 za a raba su tsakanin kamfanonin shirya aikin Hajji masu zaman kansu guda bakwai.
Hukumar ta tabbatar da cewa za a raba ƙarin guraben cikin gaskiya da adalci, tare da bin ƙa’idojin Najeriya da na ƙasar Saudiyya.
Wannan ci gaba ya zo ne makonni bayan da Saudiyya ta fara kin amincewa da buƙatar Najeriya na ƙarin guraben, bisa dalilan ƙarancin wurare da kuma matsalolin gine-gine a wuraren ibadar Hajji.
