Dr. Sokonte Davies, ɗan siyasa kuma abokin siyasar tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya fice daga jam’iyyar ADC, inda ya koma jam’iyyar APC.
Davies, wanda ya nemi takarar gwamnan Rivers a ƙarƙashin ADC, ya bayyana komawarsa APC a wata sanarwa da ya aikewa jaridar Vanguard ranar Laraba.
Ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne bayan tuntubar iyalansa, abokan siyasa da dattawa, tare da ganin cewa jam’iyyar ce za ta ba shi damar wakiltar al’ummarsa da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban Jihar Rivers.
Davies ya kuma bayyana aniyarsa ta mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake zaɓensa a 2027, tare da yin aiki wajen ƙarfafa APC daga matakin unguwa zuwa ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa.
Ya gode wa shugabannin ADC bisa damar da suka ba shi, yana mai cewa ba ya da wata ƙiyayya da jam’iyyar, domin a cewarsa, “siyasa kasuwa ce ta ra’ayoyi.”
