Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta sanar da rufe dukkan filayen wasanni da cibiyoyin wasanni da ke ƙarƙashinta na kwana ɗaya, wato Alhamis 8 ga Oktoba 2026, domin nuna alhini da girmama marigayi Sakataren Hukumar, Dr. Bashir Ahmad Maizare.
A sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ashiru Rabiu Gidan Tudu, ya fitar, ya bayyana cewa Shugaban Hukumar, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, ne ya bayar da wannan umarni bayan kammala sallar jana’izar marigayin.
Tukur Babangida ya bayyana rasuwar Dr. Bashir Ahmad Maizare a matsayin babban rashi ga Hukumar Wasanni ta Kano, Gwamnatin Jihar Kano da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai jajircewa, kishin aiki da sadaukar da kai wajen bunƙasa wasanni, inda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin hukumar tare da riƙe muƙamin Daraktan Wasanni kafin daga bisani ya zama Sakataren Kano Pillars FC daga shekarar 2012 zuwa 2013.
Ma’aikatan Hukumar Wasanni ta Kano sun bayyana alhininsu bisa wannan babban rashi, suna yabawa irin gaskiya, tawali’u da jajircewar marigayin wajen gudanar da aikinsa.
Shugaban hukumar ya miƙa ta’aziyya ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, iyalan marigayin da daukacin al’ummar jihar, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.
