Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta ce jam’iyyun siyasar da aka samu suna gabatar da ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar ’yan jam’iyyar da suka miƙa wa hukumar, ba za su samu damar tsayar da ’yan takara a zaɓen 2027 ba.
INEC ta bayyana hakan ne bayan da kotun ƙoli ta dawo da wasu tanade-tanaden dokar zaɓe na 2026 da suka shafi rajistar ’yan jam’iyyu da kuma tsarin zaɓen fidda gwani.
A ƙarƙashin sashe na 77(5) da 77(6), jam’iyyu dole ne su yi amfani da rajistar ’yan jam’iyyar da suka gabatar wa INEC wajen gudanar da zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyya da sauran zaɓukan cikin gida, haka kuma, sashe na 77(7) ya tanadi cewa jam’iyyar da ba ta gabatar da rajistar ’yan jam’iyyarta yadda doka ta tanada ba, ba za ta iya tsayar da ɗan takara a zaɓe ba.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ta samu takardar sahihin kwafin hukuncin kotun koli kuma tana nazarin abin da hukuncin ya ƙunsa domin sanin yadda za’a aiwatar da shi gabanin zaɓen 2027.
Wannan hukunci ya biyo bayan wata ƙara da jam’iyyar Zenith labour party, ZLP, ta shigar kan tanade-tanaden dokar, inda kotun ƙoli ta yanke hukunci a ranar 24 ga Satumba, 2026, tare da dawo da sassa na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na dokar zaɓen 2026.
