Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Sunusi ya kafa wani babban kwamiti da zai bincika zargen da al’ummar kauyen Waja a garin Fagam na karamar hukumar Gwaram ke yiwa hakiminsu na kwace musu gonaki da kuma lafta musu harajin da ya fi karfinsu.
Wannan ya biyo bayan rahoton Premier Radio a wannan rana ta Asabar, wanda al’ummar Fulani dake garin suka zargi hakimin nasu mai suna Auwalu Adamu da kwace musu gonaki, dora musu haraji mai yawa da kuma sayar da burtuloli da makiyaya, abinda ya jefa su da dabbobinsu cikin mummana hali
A tattaunawarsa da wakilinmu Kabir Bello Tukur da sakataren masarautar Dutse, Amadu Malami Dutse yace mai martaba sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Sunusi ne da kansa ya bada umarni kafa kwamitin, wanda za’a kaddamar da shi a ranar litinin mai zuwa a fadar sarkin Dutse da karfe 11 na safe
