Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce ya goyi bayan matakin da jam’iyyar NDC ta yanke na keɓe tikitin takarar shugaban Najeriya a 2027 zuwa yankin Kudancin ƙasar, duba da cewa matakin ya nuna yadda jam’iyyar ke raba madafun iko da kuma tabbatar da adalci.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya yi jawabi ga wakilai da magoya bayansa da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da magoya bayan jam’iyyar su wayar da kan al’umma game da manufofin jam’iyyar a yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Kalaman nasa dai na zuwa ne jim kaɗan bayan da jam’iyyar ta NDC ta amince da miƙa tikitin takarar shugaban ƙasar a shekarar 2027 a Kudancin Najeriya na tsawon shekaru huɗu kawai.
