Gwamnan ya ce kuɗaɗen na tafiya ne wajen gyara da kula da muhimman kayan aikin ruwa, ciki har da bututan ruwa da suka lalace da kuma na’urorin tace ruwa, domin tabbatar da ci gaba da samar da ruwa mai tsafta.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki samar da ruwan sha a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwa da take baiwa fifiko domin inganta lafiyar jama’a da walwalar al’umma.
Gwamnan ya amince cewa har yanzu ana fuskantar ƙalubale wajen biyan bukatar ruwa saboda ƙaruwar jama’a da faɗaɗa birane da kauyuka, amma ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da faɗaɗa ayyukan ruwa domin ƙara yawan samarwa da inganta ayyukan.
Haka kuma, gwamnatin ta ce za ta ci gaba da zuba jari a ɓangaren ruwa domin tabbatar da ɗorewar samar da tsaftataccen ruwan sha a faɗin jihar.
