Jam’iyyar Nigeria ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na zaɓen shekarar 2027 ga Kudancin Najeriya, domin wa’adin mulki guda ɗaya na shekaru huɗu.
An cimma matsaya ne bayan amincewa da ƙudurin da Afam Victor Ogene, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ogbaru ta jihar Anambra, ya gabatar a babban taron jam’iyyar na ƙasa.
Haka kuma, an amince da cewa bayan kudancin Najeriyar ya kammala wa’adin shekaru huɗun, za’a mayar da tikitin takarar shugaban ƙasar kai tsaye zuwa Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa matsayar jam’iyyar ta NDC ta buɗewa Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, da sauran ‘yan takara daga Kudancin ƙasar damar sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar kafin zaɓen fidda gwani.
A baya-bayan nan ne Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, suka koma jam’iyyar ta NDC, inda ake saka ran mutanen biyu za su jagoranci tutar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
