Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin kafa rundunar ‘yan sandan jiha, domin ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta tsaron al’umma da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Kwamitin haɗin gwiwa kan yaƙi da shan da Safarar Miyagun Ƙwayoyi Kano.
Gwamnan ya ce rundunar ‘yan sandan jiha za ta yi aiki ne tare da Rundunar ‘yan Sandan Najeriya, ba wai domin maye gurbinta ba, inda ya ce rundunonin biyu za su haɗa kai wajen kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da doka da oda, inganta tattara bayanan sirri da kuma gaggauta ɗaukar mataki kan barazanar tsaro domin ƙarawa jama’a kwarin gwiwa.
Gwamna Abba ya ce Kano na da ingantattun hukumomi, isassun ma’aikata wadanda da za su ba ta damar kafawa da gudanar da rundunar ‘yan sandan jiha da zarar an kammala gyaran kundin tsarin mulki da sauran dokokin da suka dace.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da marawa duk wata halastacciyar hanya domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya, tare da samar da yanayin da al’umma za su gudanar da harkokin kasuwanci, ilimi da rayuwar yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
