Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Shehi Shehi Maihula, tare da wasu manyan malamai, sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa Murtala Sule Garo, a wa’adi na biyu a shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Mustapha Muhammad ya fitar, inda ta ce malaman sun nuna goyon bayan ne yayin wata jerin ziyara da Gwamna ya kai wasu wuraren Mauludi guda 8 a faɗin Kano.
Sanarwar ta ce ziyarar ta fara ne a Zawiyyar Sheikh Sharif Sani, inda Gwamnan ya bayyana ayyukan more rayuwa da gwamnatinsa ta kammala da kuma waɗanda take ci gaba da gudanarwa domin inganta rayuwar al’umma.
Sheikh Sharif Sani ya yaba da ayyukan tare da yiwa Gwamnan addu’ar samun nasarar komawa wa’adi na biyu domin ci gaba da ayyukan ci gaban jihar.
A hedikwatar ɗarikar Ƙadiriyya ta Afirka da ke Kabara kuwa, jagoran ɗarikar, Sheikh Malam Karibullah Nasiru Kabara, ya yi alkawarin ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da kuma nasarar Gwamna Yusuf a zaɓen 2027.
Haka kuma, Sheikh Shehi Maihula, wanda shi ne shugaban Hisbah ta Kano, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan, yayin da a Zawiyyar Sheikh Shehi Aliyu Harazimi, da Zawiyyar Sheikh Yanmota da Sheikh Salga, aka yiwa gwamnatin addu’o’in samun nasara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa a Zawiyyar Sheikh Atiku kuwa, wadda ita ce ta ƙarshe a ziyarar, Khalifan ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Yusuf tare da yin alkawarin ci gaba da yi masa addu’a domin samun nasarar wa’adin na biyu.
