Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, tare da jinjinawa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta ce Gwamna Yusuf ya bayyana Shettima a matsayin ƙwararren ɗan siyasa, gogaggen mai gudanar da mulki kuma jagora mai hangen nesa, inda ya ce jarumtakarsa, da kishin yiwa al’umma hidima, yana mai cewa ƙwarewar sa a harkokin mulki na ci gaba da zama babbar kadara ga gwamnatin Shugaba Tinubu.
Gwamna Abba ya ce tarihin hidimar Shettima, musamman lokacin da yake gwamnan jihar Borno, da lokacin da yake Sanata a majalisar Dattawa da kuma matsayinsa na yanzu, ya nuna irin jajircewarsa wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yabawa da basirar Shettima, kishi da ƙoƙarinsa na ƙarfafa haɗin kan ƙasa da bunƙasa tattalin arziƙi, inda ya roƙi Allah ya ba shi lafiya, da hikima domin ci gaba da yi wa Najeriya hidima.
